A safiyar 26/ Ramada/1444 daidai da 17/April/2023
. Kwamitin tafsir na kungiyar jama'atul izalatil bid'a wa ikamatus Sunnah reshen zaria da sabon gari.
Sun Kai ziyara ga Mai martaba sarkin zazzau Ambasada Mal. Ahmad Nuhu Bamalli (CFR) a fadarsa Dake birni zaria.
Tawagar kungiyar dai tahada da sheikh Prof. Umar Muhammad labdo, Sheikh Muhammad Sani gumi, sheikh Dr. Sha'aibu Rabi'u imamud da'awa (shugaba kwamitin tafsir), sheikh Abubakar Bala Mai kada, sheikh Abbas salihu P.z 'Yan Agajin kunagiyar ta JIBWIS da sauran malamai.
Haka zalika tawagar ta wuce fadar hakimin Bomo Alh. Mannir Ja'afaru madakin zazzau Dan kai masa ziyarar sada zuminci a wannan lokacin watan azumin Ramadan.
Tawagar kungiyar ta izala ta Ziyarci Hajiya Aisha kwamared saikul wadda akafi sani da (Hajiya Kaka) agidanta Dake (G.R.A) zariya
Allah karba Mana aiyu kannamu gabadaya
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Mas'ud Bala Chikaji. Chairman jibwis social media sabon gari zaria.